Connect with us

Labarai

Yau ake cika shekara daya da mutuwar Umar Sa’idu Tudun-Wada

Published

on

Tsohon Mataimakin shugaban rukunin tashoshin freedom rediyo, Mallam Umar Saidu Tudunwada, ya rasu a ranar 30 ga watan Yunin 2019.
Marigayi Tudunwada ya rasu ranar Lahadi daga kan hanyarsa ta komawa Kano daga Abuja, bayan da ya halarci wani taron kungiyar kafafen yada labarai.
Tsohon mataimakin shugaban rukunin gidajen rediyon na freedom, ya yi hatsarin mota ne a yankin karamar hukumar Kura ta jihar Kano.
Marigayi Umar Said Tudun wada ya  dauki shekaru yana matsayin Janar Manaja na gidajen rediyon Freedom, inda daga bisani ya kasance daraktan yada labaran tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.
A yau ne aka gudanar da taron addu’o’i na tunawa da marigayin a dakin taro na fadar gwamnatin Kano,wato Coronation Hall.
ya rasu ya bar mata 3 da yaya da jikoki da dama.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!