Labarai
Yawan ambaliyar ruwa ke haddasa karancin abinci – Masani
Wani masanin harkokin Noma anan Kano ya alakanta matsalar karancin abinci da yawan samun ambaliyar ruwa a gonaki da ake yi.
Masanin harkokin Noman ya kuma alakanta rashin hadin kan manoma da cewa na daya daga abinda ke kawo koma baya ta bangaren bunkasar noma.
Dakta Munir Muhammad Yawale ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da wakiliyarmu Safara’u Tijjani Adam a wani bangare na bikin ranar abinci ta duniya da ake gudanarwa a yau.
Dakta Munir ya ce kamata yayi manoma su rika lura da yanayin gonar su kafin su yi shuka domin kiyaye abkuwar ambaliyar ruwan.
Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware ranar 16 ga watan oktobar kowacce shekara a matsayin ranar abinci ta duniya, sai a biyo mu nan bada kadan don jin cikakken rahoton.
You must be logged in to post a comment Login