Kiwon Lafiya
Yawan jam’iyyun a Najeriya ka iya janyo matsaloli yayin zabe-INEC
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce yawan jam’iyyun siyasa a kasar zai iya haddasa matsaloli da dama ga babban zaben kasa da za a yi a shekarar badi.
Babban mai baiwa shugaban hukumar ta INEC shawara ta kwararru farfesa Bolade Eyinla ne ya bayyana haka yayin wani taron bita da cibiyar horas shugabanci da dabarun mulki da ke Kuru Jihar Filato ta shirya jiya a Abuja.
Ya ce akwai damuwa matuka ganin yadda ake kara samun sabbin jam’iyyun siyasa, yana mai cewar a yanzu haka akwai jam’iyyu masu rajista sittin da takwas.
Farfesa Bolade Eyinla ya kuma ce a yanzu haka akwai kungiyoyi sama da dari da ke neman a yi musu rajista domin zama sababbin jam’iyyun siyasa.
Ya kara da cewa idan jam’iyyu sittin da takwas suka tsayar da ‘yan takara kaga kenan za a samu wakilan jam’iyyu sittin da takwas a rumfunar zabe wanda hakan a cewar sa zai kawo matsala ga ingancin zabe.