Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yawan roko ne ke jawo mutuwar Aure- Hajiya Munira Ya’u

Published

on

Hajiya Munira Ya’u wata mai sana’ar har hada kayan kwalliya mata da suka haɗar da sabulu da man shafawa hoda da sauransu wadda ta shafe shekaru fiye da goma tana sana’a.

Munira Yau ta bayyana cewa yawan tamabayar miji kudi bukatun yau da kullum ke jawo mace Mace aure.

Ta ce, kamata yayi ko wace mace ta nemi sana’ar dogaro da kai domin rufawa kanta asiri ba sai ta jira miji ya mata ba.

Inda ta kara da cewa ta fara sana’ar ta da kudi ƙalilan da bai wuce Naira dubu goma ba inda a yanzu a rana take kayan fiye da miliyan daya ana kai mata kasuwa .

Ta kuma ce, babban kalubale da take fuskanta shine yadda idan ta dauki mace ta koya mata sana’a daga baya ta dawo tana cin dunduniyar ta.

Hajiya Munira Ya’u, ta ce aƙalla yanzu tana da yara a karkashin ta da suka kai yawan 50 wanda suke mata aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!