Labarai
Yawancin waɗanda suka soke ni a baya sun koma APC- Wike

Tsohon gwamnan jihar Rivers, kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka soke shi a baya, yanzu sun koma jam’iyyar APC, jam’iyyar da shi ma yake cikinta a halin yanzu.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Abuja, inda ya ce lokaci ne ya tabbatar da cewa siyasar sa ta gaskiya ce ba ta son zuciya ba.
Ya ce, mutanen da suka zarge shi da cin amanar jam’iyyar PDP yanzu su ne suka rungumi APC da hannunsu biyu-biyu.
Ministan ya kuma jaddada cewa siyasa ta na buƙatar fahimta da aiki don ci gaban kasa, ba wai yin suka kawai saboda banbancin jam’iyya ba.
A cewarsa, Lokacin ya nuna waye mai gaskiya da kuma wanda yake wasa da hankalin jama’a.
You must be logged in to post a comment Login