Connect with us

Labarai

Yemi Osinbajo ya bayyana Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo abun koyi

Published

on

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana malamin addinin Islaman nan da ke jihar Filato wanda ya ceci rayukan wasu mabiya addinin kirista da ‘yan bindiga suka biyo, Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo kuma abun koyi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun shugaban kasa Laolu Akande.

Sanarwar ta ce Osinbajo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Limamin wanda ya kai ziyara fadar shugaban kasa a jiya Alhamis.

A ranar 23 ga watan Yunin bara ne Imam Abdullahi Abubakar limamin masallacin kauyen Yelwan Gindin Akwati a yankin karamar Hukumar Barikin Ladi a jihar Filato ya boye mutanen a masallacin sa bayan da ‘yan bindiga suka biyo su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,742 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!