Connect with us

Labarai

Covid19: Osinbajo baya dauke da cutar

Published

on

Biyo bayan gwajin da aka yiwa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo an gano cewa baya dauke da cutar Corona.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa Shawara kan harkokin siyasa Femi Ojudu ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau laraba.

LABARAI MASU ALAKA

Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19

Ganduje : zamu samar da kayayyakin aiki don yakar cutar COVID-19

Da dumi-dumi: Ganduje ya baiwa ma’aikata hutu saboda Coronavirus

A jiya talata ne Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kebe kansa biyo bayan ci gaba da yaduwar cutar Corona da ake samu a kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa ya yi mu’amala da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari wanda aka tabbatar yana dauke da cutar, a dalilin haka ne mataimakin shugaban kasa ya killace kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!