Labarai
Yemin Osinbajo ya ce ba daidai bane yadda ake siyasantar da batun makiyaya da manona a kasar nan
Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, ya ce; ba daidai bane wasu su rika siyasantar da batun rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoma a kasar nan.
Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana hakan ne yayin wani taron addu’a domin tunawa da ranar mazan jiya ta bana wanda aka gudanar a cibiyar kiristoci ta kasa da ke Abuja.
Ya ce, duba da irin kashe-kashe da ke abkuwa tsakanin makiyaya da manoma a baya-bayan nan, ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari umurtar jami’an tsaro na sojoji da ‘yan-sanda da su kara kaimi wajen shawo kan matsalar.
A cewar sa, ka da al’ummar kasar nan su yarda su kuma fadawa tarkon ‘yan-siyasa da masu ci da addini wadanda suka siyasantar da batun rikicin Boko-Haram a shekarun baya.
Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa lokaci yayi da ‘yan Najeriya za su rika aiki tare domin magance matsalar tsaro, yana mai cewar, ba daidai bane al’ummar kasar nan su rika bari ‘yan-siyasa suna amfani da su domin biyan bukatun kansu.