Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yerima: Sojoji sun kashe ƴan bindiga 53 a jihar Zamfara

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarun shiyya ta takwas ta rundunar karkashin shirin operation tsare mutane, sun kashe ƴan bindiga guda hamsin da uku yayin wani gumurzu da su ka yi a baya-bayan nan a jihar Zamfara da wasu jihohi da ke makwabtaka da jihar.

 

Mai magana da yawun rundunar burgediya janar Muhammed Yerima shine ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya lahadi.

 

Sanarwar ta ce cikin ƴan bindigar hamsin da uku da rundunar ta kashe har da kwamandoji guda biyar.

 

A cewar sa, yayin bata kashin sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutane goma sha takwas wadanda ƴan bindigar su ka yi garkuwa da su.

 

Haka kuma sanarwar ta ce sojojin sun lalata maboyar ƴan bindiga a dazukan Jaya, Kadaya da kuma Bayan Ruwa.

 

Burgediya janar Muhammed Yerima ya kara da cewa sojojin sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda 8 da bindiga kirar machine gun, ba ya ga wasu makaman masu tarin yawa.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!