Labarai
Yerima ya tsallake rijiya da baya, bayan zargin yunkurin kai masa hari

Wasu rahotanni daga Najeriya sun ce sojan da ya yi cacar baka da ministan Abuja, Laftanar Ahmed Yerima ya tsallake rijiya da baya da yammacin ranar Lahadi, inda wasu mutanen da ake zargin mahara ne suka yi ƙoƙarin kai masa hari.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wata majiyar soji ta tabbatar mata da cewar wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin wasu motoci ƙirar Hilux guda biyu da basu da lamba sun yi ta bibiyar Yarima daga gidan man NIPCO a kan hanyar Gado Nasco da ke birnin tarayya Abuja.
Majiyar ta ce sojan ya zargi cewar ana bin sa, sai ya yi domin kauce musu da misalim karfe 6.30 na yamma, abinda ya kai ga shaidawa hukumomin su na soji.
Wannan lamari na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan cacar bakan da sojan ya yi da ministan Abuja Nyesom Wike a kan wani fili da tsohon babban hafsan sojin ruwa na ƙasa ya mallaka a ƴankin Gaduwa.
You must be logged in to post a comment Login