Kasuwanci
Yiwa Twitter rijista a Najeriya zai ƙara samar da kuɗaɗen shiga – FIRS

Hukumar tattara haraji ta ƙasa FIRS ta ce, da zarar an yiwa kamfanin Twitter rijista a Najeriya za a ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Hukumar ta ce, idan aka yiwa Twitter da sauran dandalin sada zumunta rijista a ƙasar nan, kuɗaɗen haraji za su ƙaru zuwa tiriliyan biyar a shekarar 2022.
Shugaban hukumar Mohammed Naami ne ya bayyana hakan, lokacin da ya bayyana a gaban kwaamitin majalisar wakilai a Abuja.
Labarai masu alaƙa:
Muna buƙatar samun harajin sama da Tiriliyan 10 a 2022 – FIRS
Muhammad Naami ya ce, ya ce, a shekarar 2022 hukumar ta yi hasashen samun harajin naira tiriliyan 10 da biliyan ɗaya, adadin da ayke nuna cewa an samu ƙarin naira tiriliyan biyar akan harajin da aka samu a bana.
You must be logged in to post a comment Login