Labarai
Yobe: Mutum 1 ya rasu 16 kuma sun jikkata a hatsarin mota

Mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu mutane goma sha shida suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a karamar hukumar Karasuwa, ta jihar Yobe.
Shaidu sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon irin tseren ganganci da direban motar ya yi, lamarin da ya jawo ta kauce daga hanya.
Hukumar kiyaye haddura ta ƙasa, ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta ce tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa.
Hukumar ta kuma yi kira ga direbobi da su rika bin ƙa’idojin hanya, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login