Labarai
Yunƙurin tsige ni ƙaddara ce a rayuwata – Ibrahim Khalil
Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce yunƙirin tsige shi wata ƙaddara ce a rayuwar sa.
Malamin ya bayyana hakan a lokacin da kwamitin ƙoli kan harkokin addinin Musulunci na ƙasa ya kai masa ziyara.
Malam Ibrahim ya ce, yunƙurin tsige shi da wasu suka yi ƴar manuniya ce ta samun ɗaukaka da nasara.
“Wannan yana nuna jarrabawa daga wajen Ubangiji kuma akwai buƙatar mutum ya ƙara tuba idan irin wannan lamari ya taso”.
Majalisar malamai ta Kano ta sake jaddada mubaya’arta ga Sheikh Ibrahim Khalil
“Duk ba wani abu muke yiwa fafutuka ba, face addinin musulunci, don haka wannan ba sabon abu ba ne matuƙar aka ce mutum zai yi wa’azi a cikin al’umma”.
Malam Khalil ya ci gaba da cewa “Abin alfahari ne haɗin kan da aka samu a kwamitin duk da wasu sun yi gaban kan su, amma wannan ya ƙara haska mana fitila”.
Wannan dai na zuwa makwanni kaɗan bayan da wani tsagi na majalisar ya ayyana tsige Malam Ibrahim Khalil.
You must be logged in to post a comment Login