Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar malamai ta Kano ta sake jaddada mubaya’arta ga Sheikh Ibrahim Khalil

Published

on

Majalisar malamai ta jihar Kano ta sake jaddada mubaya’arta ga Sheikh Ibrahim Khalil a matsayin shugaban majalisar.

Yayin wani taro da majalisar ta gudanar a ranar Talata da shugabanninta ta yi Allah wadai kan yunƙurin da wasu da ba ƴaƴan majalisar ba suka yi na bada sanarwar tsige Malamin.

Farfesa Muhammad Babangida Muhammad shi ne mataimakin sakataren majalisar ya ce “An kafa wannan majalisar a  shekara ta 1981 amma akwai wadanda ba su taɓa halartar taron majalissar ba, kuma har kawo yanzu waɗanda suka fitar da wannan sanarwa sun kasa bayyana kan su, a matsayinsu na ƴan cikin majalisar, sai dai mun fahimci suna son tayar da ƙura a majalissar”.

“Abin takaici ne ace wasu ƴan tsirarun malamai su ayyana wani sabon shugaba a majalisar, a don haka muna jadda mubaya’ar mu ga Malam Khalil a matsayin shugaba, kuma muna kiran sa ya ƙara kan jajircewar da yake  akan shugabancin majalissar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani tsagi a majalisar ya ayyana tsige Malam Ibrahim Khalili a matsayain shugaban majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!