Labarai
Za a ɗaga matsayin tashar wutar lantarki ta jihar Yobe
Gwamnatin tarayya za ta ɗaga matsayin tashar wutar lantarki ta jihar Yobe ta yadda wuta za ta wadaci al’ummar jihar.
Ministan lantarki na ƙasa Injiniya Abubakar Aliyu ne ya bayyana hakan ranar Labara yayin ziyarar gani da ido a babbar tashar lantarki ta jihar Yobe da ke Damaturu.
Ministan wanda ya samu wakilcin Injiniya Sule Abdulazeez shugaban kamfanin raba wutar lantarki na kasa TCN, ya ce za a ɗaga matsayin tashar ne, domin ƙaruwar buƙatarta ga al’umma.
Ya ce “An bada kwangilar samar da na’urar da za ta ƙara yawan wutar lantarki mai karfin Volt-Amps (MVA) miliyan 150 a wannan tasha”.
Injiniya Abubakar Aliyu ya yabawa hukumomin tsaro saboda ƙoƙarinsu wajen samar da tsaro ga tashar wutar lantarkin.
Ministan yayi kira ga jama’ar da ke kusa da tashar lantarkin da su riƙa sanya idanu game da ita.
A watan Fabrairun shekarar 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da tashar wutar lantarkin ta Damaturu.
You must be logged in to post a comment Login