Labarai
Za a Buɗe Makarantu a Jihar Naija Makonni Kaɗan Bayan Rufe Su

Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umar Bago, ya amince da sake buɗe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar, bayan an ceto daliban ma’aikatar St. Mary da aka sace a Papiri a karamar hukumar Agwara ta jihar.
A wata sanarwa da Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Dakta Hadiza Asebe Mohammed ta fitar, ta ce bude makarantun zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Janairun da muke ciki.
Ta kara da cewa makarantun da ke yankunan da har yanzu ake ganin ba su da isasshen tsaro ba za a bude su ba.
Sanarwar ta ce ana ci gaba da tantance dukkan makarantu domin tabbatar da lafiyar dalibai da malamai kafin ranar da aka tsara.
Gwamnatin jihar ta rufe makarantu ne tun bayan sace kimanin ɗalibai da ma’aikata 230 a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, lamarin da ya tilasta dakatar da jarrabawar zangon farko da kuma rufe manyan makarantu na ɗan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login