Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da dumi-dumi :An rufe makarantu a jihar Zamfara

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun firamare da sakandire a kananan hukumomin jihar 14.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya bada umarnin, biyo bayan wani harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen KAAYA a ƙaramar hukumar maradun da safiyar yau Laraba, tare da yin garkuwa da dalibai.

Kwamishinan yan sandan jihar Ayuba Elkana ne ya tabbatar da hakan yayin zantawar sa da manema labarai.

Ya ce, makarantun za su kasance a rufe har zuwa lokacin da al’amuran tsaro za su daidaita.

Ayuba ya kuma ce, har yanzu ba a kai ga gano adadin yaran da aka sace ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!