Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Za a fara kama masu sai da gurbatacciyar zuma a Najeriya

Published

on

Kungiyar masu kiwon zuma ta kasa wato Apicultural society of Nigeria, ta ce, za ta dauki tsauraran matakai kan masu sayarwa jama’a gurbatacciyar zuma.

A cewar kungiyar ba daidai bane wasu su rika cutar da jama’a wajen sayar musu da gurbatacciyar zuma.

Shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Salisu Adamu Giginyu ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom Rediyo a yau Litinin.

Ya ce, kungiyar, ta sha samun irin wadannan labari na damfarar jama’a ana sayar musu da zuma gurbatacciya, saboda haka ya sa kungiyar ta shawarci jama’a da su rika sayan zuma a wajen mambobin kungiyar wadanda su ke da rajista.

“Muna da shaida wadda duk mamba na wannan kungiya an bashi ID Card wanda shine shaidar sa wanda idan ya sayarwa da wani mutum zuma marar kyau zamu iya ganoshi a kamashi domin bi wa mutumin hakkinsa”.

NAFDAC ta kama jabun magunguna

Lagos:kudan zuma sun kashe wani jami’in hukumar yaki da fasakwauri

“Idan mutum ya je zai sayi zuma ya tambayi mai sayar da zumar Ina katin shaidarsa idan ya nuna a bincika a gani hoton sa ne a jiki daganan Kuma sai a duba bayan kati akwai lambar rijista idan duk ya cika wadannan kaidoji za a iya sayan zumar amma fa Kar a shanye zumar gaba daya bayan an saya a dan rage komai kashinta wanda ita za ta zama hujja ko da daga bisani an gano cewa zumar gurbatacciya ce” Inji kwamared Giginyu.

Haka zalika Kwamared Giginyu ya ce matukar aka sayi zumar a hannun dan kungiya sannan aka ga an gurbatata to a Kira daya daga cikin wadannan lambobi:08038022660, 08035645774 uwar kungiyar za ta bincika ta dauki mataki.

Shugaban kungiyar masu kiwon zuma ta kasar dai ya yi wannan jawabi ne biyo bayan kama wasu masu gurbata zuma da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi a makon jiya.

Rahotanni sun ce a Najeriya kaso mafi yawa na zuma da ake sayarwa jama’a an gurbatata.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!