Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An yi hatsarin mota har sau uku a titin Sharada

Published

on

Da farko dai wata mota ce da tayarta ta fashe ta abkawa matafiya a daidai Kai-da-Kafa kusa da kwanar Freedom

Shaidun gani da ido sun ce tun farko direbar motar na cikin tafiya ne sai kawai tayar motar ta fashe inda Kuma ya kasa shawo kan motar wanda sakamakon haka ya abka kan wani babur da Kuma wani Mutum da ke tafiya a gefen titi.

Wani wanda lamarin ya faru akan idon sa mai suna Sammani Aliyu, ya ce mutumin da motar ta buge ya samu mummunan rauni a kafarsa

Haka zalika da misalin karfe daya da mintuna hamsin wani hatsarin na biyu ya abku inda wani direbar mota ya abkawa wani babur din Adaidaita Sahu.

Yayin da hatsarin na uku ya faru daf da shalkwatar hukumar Hisba da ke Unguwar Sharada inda wata motar safa ta abkawa wata mota kirar Honda da ke kokarin juyawa.

Da ya ke zantawa da freedom Rediyo direbar motar da aka yiwa barnar Aminu Ibrahim ya ce ya fito ne daga wani garejib gyaran motoci da ke Danagundi don yin gwajin motar bayan ya tsaya yana jira zai Sha kwana kawai sai ya ji an dakeshi ta baya wanda sanadiyar hakan shima ya abkawa wata mota da ke gabanshi.

“Wannan motar gwamnati da kake gani ta dauko dalibai ita ce ta yi mini barnar Kuma direbar ya karbi laifin sa yanzu zamu je gareji ne domin motar ba tawa bace.” Inji Aminu Ibrahim.

Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon kazamin hatsarin mota a Kano

Jigawa:mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota

Ko da freedom Rediyo ta tuntubi direbar motar don jin ta bakinsa ya ce duk abinda waccan wanda aka yi asarar motar ya fada gaskiya ne amma ba zai kara kan haka ba.

A nasa bangaren shugaban kungiyar masu tuka motocin daukar dalibai ta gwamnati, Kabiru Ali Jibril ya ce, za su kai motar gareji don tattaunawa da mai motar don jin ta bakinsa.

Freedom Rediyo ta tuntubi mai magana da yawun hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa Kabiru Daura ta wayar tarho, ya ce ya zuwa lokacin labarin faruwar lamarin bai Kai gareshi ba.

Sai dai a nata bangaren hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta Sa’id Muhammed Ibrahim, ta ce, hatsarin farko da ya faru a kusa da kwanar Freedom, an kirasu a waya an sanar dasu.

Kafin jamiansu su karasa wajen da lamarin ya faru, tuni aka dauki wadanda suka jikkata aka kaisu a Asibiti yayin da Kuma sun tura da jami’an su zuwa wajen hatsarin na biyu wanda ya faru a kusa makarantar nazarin muhalli ta jihar Kano sun dauki wadanda lamarin ya shafa zuwa Asibiti.

Amma kuma ya ce ba a samu rasa rai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!