Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Abinda yasa EFCC zata binciki Kwankwaso da wasu mutane

Published

on

Hukumar ya ki da cin hanci da rashawa ta  kasa EFCC, zata binciki tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa kan zargin karkatar da kudin makamai sama da biliyan 35.

Daga cikin wanda hukumar ta EFCC, zata bincika har da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya na  zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ,Chief Mike Oghiadomhe, sai Adetekunbo Kayode, da dukkanin su tare da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya  Rabiu Musa Kwankwaso wanda yana rike d amukamain ministan tsaro a wancan lokaci kan   karkatar da sama da biliyan 35, na kudaden siyan makamai da kwantiragin siyo su.

Jaridar Thisday ta rawaito cewa , cikin wadanda  hukumar  zata bincika har da tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar tsaro Dakta Haruna Sunusi, da Manjo Janar Nguni.

Bincike ya tabbatar da cewa, kwantiragin siyo makaman anyi shi ne don samar da makamai da sauran kayan aiyyukan gudanar da tsaro ga tawagar sojin kasar nan dake aiyyukan samar da tsaro a kasashen duniya.

Siyasa: Shin ritayar da Ganduje yayiwa Kwankwaso ta tabbata?

Kwankwaso mutum ne mai son kansa-Ganduje

Shin rigimar Ganduje da Kwankwaso tazo karshe?

An dai ranto  kudaden daga ofishin lura da  basussuka na kasa wato debt Management office (DMO) don siyan makaman ga rundunar Sojin.

Kakakin hukumar ta EFCC, Mista Tony Orilade,  ya tabbatar da gudanar da binciken inda yace wasu daga cikin kwantiragin ba a kammala su ba, ya yin da wasu kuma kawai an yi shaci fadin biyan  su wanda a zahiri ba ayi ba.

Hukumar ta EFCC, ta ce zata cigaba da bincike don tabbatar da yadda aka karkatar da kudaden karkashin wani babban kamfanin kwangila, da yanzu haka suna bada hadin kai wajen gudanar da binciken.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!