Manyan Labarai
Za a fara koyar da harshen China a jami’ar Bayero
Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ce nan gaba kadan za ta fara koyar da harshen kasar China.
Jami’ar ta sanar da hakan ne a shafinta na Intanet jim kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta juna da ofishin jakadancin kasar China.
Da yake sanya hannu kan yarjejeniyar, Babban jami’i mai kula da harkokin al’adu na ofishin jakadancin China Mista LI Xuda, ya ce, jami’ar Bayero ta kafa tarihin da suka ga dacewar yin hadin gwiwa da ita don samar da irin wannan ci gaba.
Li Xuda ya kara da cewa, kafa cibiyar shakka babu za ta taimaka wajen samar da kwararru a harshen China, da hakan ka iya bunkasa alaka dake tsakanin kasashen biyu musamman ma a bangaren kasuwanci.
Da yake jawabi bayan kammala sanya hannun, Shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa mai kula da harkokin karatu Farfesa Adamu Idris Tanko cewa ya ce, jami’ar ta jima tana hada gwiwa da wasu jami’oin kasar China wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwa.
Farfesa Adamu Idris Tanko ya kara da cewa, jami’ar za ta fito da sabon tsarin koyar da harshen kasar China ga ‘yan kasuwa, don basu damar bunkasa yanayin kasuwancin su.