Kimiyya
Za a fara rajistar sabbin layukan waya da lambar NIN a ranar 19 ga Afrilu
Gwamnatin tarayya ta amince da fara rajistar sabon layin wayar tarho tare da hadashi da lambar dan kasa ta NIN.
Ministan sadarwa da bunkasa fasahar tattalin arziki Dr. Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa Dr Femi Adeluyi ya fitar.
Sanarwar ta ce, sayar da sabbin layuka da aka dakatar da yi a baya, za a ci gaba da yin-sa daga ranar 19 ga watan Maris, kamar yadda aka saba tun da fari.
You must be logged in to post a comment Login