Labarai
Za a fuskanci ruwan sama da iska mai karfi a Arewacin Najeriya- NiMet

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen cewa, daga yau Litinin zuwa Laraba za a fuskanci ruwan sama da iska mai karfi a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar da yammacin Lahadi, ta ce. jihohin da za su fuskanci yanayin sun hada da Kebbi da Zamfara da Sokoto sai Gombe da Borno da kuma Yobe.
Haka kuma, a cewar rahoton, za a samu mamakon ruwan sama da tsawa a jihohin Bauchi da Yobe da Jigawa sai Kano da Kaduna da Zamfara da Katsina da Adamawa sai Taraba da kuma Borno.
Hukumar ta shawarci manoma da matafiya a yankunan da abun ya shafa da su kasance cikin shiri domin guje wa hadurran da ka iya biyo bayan ruwan sama mai karfi da kuma iska.
You must be logged in to post a comment Login