Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a rufe Katsina ba shiga ba fita daga Talata

Published

on

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce daga karfe 7 na safiyar Talata mai zuwa za a rufe kwaryar birnin Katsina ba shiga ba fita domin dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Cikin jawabin da gwamnan yayi ya ce cutar na kara mamaya kuma a yanzu haka an samu mutane biyu masu dauke da cutar a birnin Katsina, a don haka ya zama tilas a rufe garin, kamar yadda aka rufe Daura da Dutsinma.

Gwamna Masari ya ce daga karfe 7 na safiyar Talata ba shiga ba fita, sai dai wuraren sayar da danyen abinci da shagunan sayar da magani.

Har ila yau, Masari ya umarcin al’ummar sauran kananan hukumomi 31 da suka zauna a kananan hukumomin su, amma babu maganar zirga-zirgar zuwa wata karamar hukumar.

Izuwa yanzu mutane 12 ne suka kamu da cutar Coronavirus a jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!