Coronavirus
Covid-19: An cafke mutum 62 da suka shigo Sokoto daga Legas
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta cafke wata babbar mota makare da mutane 62 da ta shigo jihar daga jihar Legas, dukda dokar hana shiga da fita daga jihar da gwamnati ta sanya.
Mai baiwa gwamnan Sokoto shawara kan hukumar tsaro da gyaran gari ta Marshal Bello Malami Tambuwal ne ya bayyana hakan, a yayin zantawarsa da wakilin mu Umar Ahmad Baffa.
Bello Malami ya ce sannan sun kama wata mota wadda ita ma ta shigo jihar daga jihar Kebbi, sannan cikin mutanen da aka samu akwai ‘yan jihar ta Sokoto da kuma ‘yan jamhuriyyar Nijar.
Gwamnatin Sokoto dai ta sanya dokar hana shiga da fita daga jihar domin dakile yaduwar annobar Corona.
Har izuwa yanzu dai ba a samu bullar annobar a jihar ba, sai dai ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce ta samu kiraye-kiraye daga al’umma kan wadanda suke zargin sun kamu da cutar.
Sannan tuni sun dauki jinin mutane 18 daga ciki kuma duka sakamakon su ya nuna cewa basa dauke da cutar.
Karin labarai:
You must be logged in to post a comment Login