Connect with us

Labarai

Za mu ƙara ƙarfafa alaƙa da kasashen Sin da Faransa- Gwamna Abba Kabir

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudurin gwamnatinsa na ƙarfafa alaƙa da kasashen Sin da Faransa a matsayin wata hanya ta jawo ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar ba-zata zuwa manyan makarantun koyon harsunan guda biyu da ke garin Kwankwaso, a karamar hukumar Madobi, inda ake koyar da harsunan Sinanci da Faransanci.

Makarantun dai an kafa su ne tun a lokacin mulkin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, da nufin haɓaka kwarewar ɗalibai a harsunan kasashen ketare, musamman Sinanci da Faransanci.

Sai dai makarantun sun fada cikin halin kunci da lalacewa, sakamakon rashin kulawa da aka nuna a lokacin gwamnatin da ta gabata, karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, Gwamna Abba ya nuna damuwa game da yadda aka bar makarantun suna rushewa, ya na mai yin alƙawarin daukar matakan gaggawa domin farfado da su.

Gwamnan ya kuma ce, gwamnati za ta gyara kuma ta sake amfani da makarantun yadda ya kamata, domin amfanar matasan Kano da kuma bunkasa sha’anin ilimi a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!