Labarai
Za mu ɗaukaka ƙara kan hurumin kotu na rushe shugabancin Abdullahi Abbas – Ganduje
Gwamnatin Kano ta ce za ta ɗaukaka kara a kan hukuncin da kotu a Abuja ta yi na rushe zaɓen tsagin gwamna Ganduje da aka yi na shugabannin jam’iyyar APC a nan Kano.
Kwamishinan shari’a Barista Musa Abdullahi lawan ne ya bayyana hakan a yau yayin ganawa da manema labarai, jim kadan bayan da kotun ta sanar da hukuncinta kan zaɓen.
Barista Musa Lawan ya ce “za mu duba kundin tsarin shari’a domin ɗaukar matsaya tare da yin duba, don ganin kotun na da hurumi ko ba ta da hurumi a kan shari’ar”.
“Ko a lokacin da aka yi zaɓen mazabu na Kano a guda ɗaya aka yi, a don haka za mu duba hukuncin tare da ɗaukar mataki a nan kusa”.
A ranar Talata 30 ga watan Nuwamba wata babbar kotu a Abuja ta rushe zaɓen da aka yiwa shugaban jam’iyya APC tsagin gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje.
You must be logged in to post a comment Login