Labarai
Za mu ɗauki mataki kan masu karɓar kuɗaɗe a hannun direbobi ba bisa ƙa’ida ba- Barr. Daderi

Za mu ɗauki mataki kan masu karɓar kuɗaɗe a hannun direbobi ba bisa ƙa’ida ba- Bar. Daderi
Gwamnatin jihar Kano, ta sha alwashin bibiyar matsaloli da kuma bukatun da ƙungiyar masu Motocin haya ta Ƙasa NARTO, suka gabatar mata musamman ma na samar da wuraren ajiye manyan motoci a manyan titinan shigowa kano.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Ma’aikatar Sufuri Zaharaddeen Adamu Ibrahim Gora, ya fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ruwaito cewa, Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri Barista Haruna Isah Dederi, ne ya bayyana daukar wannan mataki yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar ta NARTO shiyyar Kano yayin da suka kai masa ziyara.
Barista Haruna Isa Dederi, ya kuma bayyana cewa Ma’aikatarsa ta samu rahoton cewa akwai wasu da ke karɓar kudade a hannun direbobi ba bisa doka da ka’ida ba,don haka za su dauki matakin kan lamarin, ya na mai jaddada yunƙurin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, na ƙoƙarin gina tsari nagari a fannin sufuri da kyakkyawar al’umma.
A nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar ta NARTO, Alhaji Salisu Ibrahim Balarabe, ya jawo hankalin Ma’aikatar kan muhimmancin samar da wuraren ajiye manyan motoci a dukkan hanyoyin shigowa Kano domin rage cinkoso da inganta tafiyar motocin cikin natsuwa tare da duba halin da tashoshin manyan mklotoci na Dakatsalle da Dawakin Kudu da sauransu ke ciki.
You must be logged in to post a comment Login