Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Za mu amince da kasafin 2022 ba da jimawa ba – Ahmad Lawal

Published

on

Majalisar dattijai ta ce, za ta amince da kasafin ƙudin 2022 kafin ƙarshen shekarar 2021.

Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar kafin shugaba Buhari ya gabatar da kasafin ƙudin 2022 a zauren majalisar dokokin ƙasar nan.

Ahmad Lawan ya ce, majalisa za ta yi aiki tuƙuru wajen ganin an fara aiki da sabon kasafin ƙudin a shekara mai kamawa ta 2022.

A ranar Alhamis ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin shekarar baɗi a gaban zauren majalisun ƙasar nan.

Kasafin kuɗin dai ya kai tiriliyan 16 da biliyan 39, kuma za a ciyo bashi domin cike giɓin kasafin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!