Labarai
Za mu buga Hotuna da Sunayen duk wanda aka samu ya ke belin masu aikata laifi a gidanjen Rediyo da Jaridu
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ingata matatar ruwa dake ƙaramar hukumar Wudil da samar da rijiyoyin Burtsatse domin samarwa da al’ummar yankin masarautar Gaya saukin matsin rashin ruwa da yankin yake fama da shi.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da safiyar yau yayin da sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Gaya ya kawo masa ziyarar barka da sallah a fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatin sa zatayi dukkan nin mai yuhuwa wajen samarwa da yankin sauki a fannin ruwa da sauran abubuwa.
Abba Gida-gida ya sha alwashin fallasa sunayen duk wadanda aka samu sun je neman belin masu aikata laifi a Kano, domin samar da tsaro da kwanciyar hankali me ɗorewa.
A nasa jawabin tun da fari sarkin Gaya Dakta Ibrahim Abubakar Gaya Ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta duba irin halin da suke ciki na rashin ruwa a yankin na Gaya domin samar musu da saukin wannan matsalar cikin gaggawa.
Haka kuma masarautar tayi kira ga gwamnati da ta samarwa da al’ummar yankin babbar makarantar gaba da sakandare domin samar musu da saukin wajen shigowa cikin birni.
You must be logged in to post a comment Login