Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ceto ɗaliban Bakura nan ba da jimawa ba – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta alƙawarta ceto ɗaliban kwalejin aikin noma da ilimin dabbobi ta Bakura da ƴan bindiga suka sace a baya-bayan nan.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Yusuf Gusau ya fitar.

Tun da fari dai gwamnatin jihar ta tabbatar da sace daliban makarantar su 15 tare da ma’aikata 4 tun a ranar Lahadin da ta gabata.

Ƴan bindiga sun hallaka wani magidanci da ƴaƴansa a Zamfara

A cewar Matawalle tuni gwamnatin jihar ta samar da tsaro a makarantun jihar tun bayan sace ɗaliban sakandiren ƴan mata ta Jangebe, kuma za ta ci gaba da tabbatar da tsaro don kiyaye faruwar hakan a gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!