Mu Ƙyaƙyata
Za mu ci gaba da bada tallafin man fetur zuwa 2022 – Buhari

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da bada tallafin man fetur a cikin watanni shida na farkon shekarar 2022.
Ministar kuɗi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wani zama da aka gudanar a taron tattalin arzikin Najeriya a Abuja.
Ta ce gwamnatin tarayya ta yi tanadin tallafin man fetur da zai isa har zuwa karshen watan Yuni na shekara mai zuwa.
Ta ƙara da cewa za a fara amfani da cikakken farashi da aka ƙayyade na harkokin man fetur da iskar gas nan da watan Yulin 2022.
You must be logged in to post a comment Login