Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ba zai cigaba da biyan tallafin man fetur ba

Published

on

Ministan man fetur na Najeriya, Timipre Sylva, ya ce gwamnatin tarayya ta cimma matsayar cewa ba za ta iya daukar nauyin tallafin man fetur ba.

Mista Sylva ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin Instagram na ma’aikatarsa.

A cewarsa bayan yin nazari sosai a kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, gwamnatin tarayya ta yanke matakin cewa ba zata iya cigaba da daukar nauyin tallafin man na fetur ba.

A cewarsa, hakan na nufin cewa gwamnati ba za ta ci gaba da samar da man fetur da sauran kayayyakin aikin da suka shafin bangaren ba, amma kuma zata karfafawa ‘yan kasuwa gwiwar su cigaba da samar da man da dangoginsa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!