Labarai
Za mu ci gaba da bayar da tallafi a fannin tsaro- Mazauna Danbare

Kungiyar ci gaban unguwar Gangar Ruwa Tudun Tsakuwa da ke yankin Dan Bare a karamar hukumar Kumbotso ta sha alwashin ci gaba da tallafawa musamman ma a harkokin tsaro don dakile aikata laifuka.
Shugaban kungiyar Nura Abdullahi Azara, ne ya bayyana hakan yau lahadi lokacin da suke mika ofishin da suka samar ga rundunar tsaro ta Civil Defence don inganta tsaro a yankin.
Ya ce, yawan iyakokin unguwar da ke kawo musu barazanar tsaro na cikin dalilan da suka sanya su samar da ofishin.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Kumbotso Abdullahi Gali Basab, cewa ƴa yi yunkurin da mazauna Yankin suka yi abu ne da ya kamata sauran unguwanni su yi koyi da shi don inganta harkokin tsaro.
A nasa jawabin, kwaamandan Rundunar tsaro ta Civil Defence na Kano Shafiu Abdulmuminu, wanda mataimakin sa Ishaq Ibrahim Abdullahi, ya wakilce shi ya ce, za su tabbatar da tsarin aikin jami’an na tabbatar da bin doka ba tare da cin zarafi ko shiga aikin da ba nasu ba.
You must be logged in to post a comment Login