Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai gwamnati ta magance ta’addanci- Arewa Mu farka

Published

on

Kungiyar Arewa Mu farka, ta sha alwashin ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana har sai Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin da ya kamata game da satar mutane da Dalibai tare da shawo kan matsalar tsaro dake damun yankin Arewacin Nijeriya.

Shugaban kungiyar Sharfaddin Bature, ne ya bayyana hakan yayi wata zanga-zanga da suka gudanar yau Litinin a jihar Kano.

Ya kuma Kara da cewar akwai rashin kishi daga yansiyasar dake wakiltar yankin Arewa a majalisu da sauran hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Shi yasa Gwamnati har yanzu bata dauki matakin kawo kareshen matsalolin ba.

Matasan na kungiyar Arewa mufarka sun cigaba da gudanar da tatakin zuwa wasu sasan na birnin Kano da nufin nuna takaicin su Kan abubuwan dake faruwa na rashin tsaro a yankin na Arewa.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!