Labarai
Za mu daina tura shanu zuwa jihohin Kudu- Gwamna Bago

Gwamnatin jihar Neja ta ce, za ta daina tura shanu zuwa wasu jihohin Kudu nan gaba kadan a wani mataki na bunkasa harkokin fannin Noma da Kiwo.
Gwamnan Jihar Nijar Umar Bago, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yin karin haske a wajen wani taron tattalin arziki da bunkasa fannin noma da ya gudana a baya baya nan a jihar Lagos.
Bago ya sanar da cewa jihar sa za ta daina kai shanu kai tsaye zuwa kasuwannin Lagos da Ogun da wasu jihohin Kudu.
A cewar gwamna Umaru Bago, hakan zai ba manoma da makiyaya damar cin moriyar amfanin da suka yi.
Haka kuma, gwamnan ya ce, jihar ta Neja za ta kara yawan filayen gona da ta ware wa jihar Lagos daga kadada 20,000 zuwa 100,000 domin kara inganta hadin kai wajen samar da abinci.
You must be logged in to post a comment Login