ilimi
Za mu dauki nauyin karatun duk mahaddacin da ke shirin yin karatun Boko- Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce, gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun duk wanda ya haddace Alƙur’ani kuma ya ke son ci gaba da ilimi a fannonin zamani kamar likitanci ko unguwanzoma da sauran fannonin ayyukan zamani.
Gwamnan ya bayyana haka ne a babban taron da aka gudanar domin gyara tsarin karatun Almajiri da Islamiyya a jihar, inda malamai, shugabannin al’umma, ƙungiyoyi da hukumomi suka halarta.
Radda ya ce, gwamnati za ta kafa sabbin makarantu guda uku da za su haɗa mahaddata Alƙur’ani da ilimin zamani irin su Turanci, Lissafi da koyon sana’o’in hannu ga yara maza da mata.
Ya kuma jaddada cewa malamai za su taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar wannan shirin, in da ya bukaci iyaye da al’umma da su bayar da goyon baya domin gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalar almajiranci ba.
Rahotonni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata.
You must be logged in to post a comment Login