Kasuwanci
Za mu dawo da karɓar harajin ƴan Adaidaita sahu- KAROTA
Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta dawo da ƙarɓar Harajin kullum-kullum na matuƙa Baburan Adaidai Sahu.
Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Injiniya Muhammad Diggol ne ya bayyana hakan, yayin da yake ganawa da ƙungiyoyin sufurin Adaidai Sahu a shalkwatartar hukumar KAROTA.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA Nabilusi Abubakar Ƙofar Nai’sa ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan ya ce, ya zama wajibi Gwamnatin ta ci gaba da karɓar harajin domin ciyar da jihar Kano gaba ta ɓangaren sufuri.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu.
Ya kuma ce, za a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙa wa direbobin biyan harajin na kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ci na matsayin rayuwa
Sanarwar ta ƙara da cewa, ya zama wajibi gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki.
A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar Kano baki daya
A nasa jawabin Shugaban Hukumar KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir ya ce, Hukumar KAROTA ta lura da yadda siyasa ta lalata ɓangaren sufuri a fadin Jihar Kano, don haka ba za su zuba ido su bar ɓaraka ta ci gaba da faɗaɗa ba, dole ne a dauki matakin ɗinke ɓarakar
Shugaban na KAROTA, ya ja hankalin ƙungiyoyin Adaidai Sahun su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin cin gajiyar tsare-tsaren da gwamnati ke shirin bijiro da shi da manufufinta na ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, Taron ya samu halartar Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Injiniya Muhammad Diggol da shugaban Hukumar KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir, da mai bai wa gwamna Abba Kabir Yusuf, shawara a ɓangaren sufuri Maisalati Garko da kuma kungiyoyin masu sana’ar tuƙa Adaidai Sahu.
You must be logged in to post a comment Login