ilimi
Za mu fara bada alawus ga ɗaliban da ke karantar fannin ilimi a jami’a da kwaleji – Buhari
Gwamnatin tarayya ta amince da fara biyan alawus ga ɗaliban da ke karantun digiri na farko a jami’o’in gwamnatin tarayya a ƙasar nan da ya kai Naira 750,00 waɗanda suke karantar fannin ilimi.
A ɓangare guda kuma za ta riƙa bai wa ɗalibai masu karatun NCE a kwalejojin tarayya alawus na naira dubu 50, 000 su ma wadanda suke karantar fannin ilimi a kowanne zangon karatu.
Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a wani ɓangare na bikin ranar malamai ta duniya ta a Abuja.
Adamu Adamu wanda babban sakatare a ma’aikatar ilimi Sonny Echono ya wakilta yayin taron da aka shiryawa malamai ya ce, ma’aikatar ilimi za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin samar da aikin yi ga ɗalibai kai tsaye da zarar sun kammala karatu.
You must be logged in to post a comment Login