Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu fara biyan ƴan fansho basukan da suke bin mu – Muhammad Garba

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware naira biliyan ɗaya domin biyan tsoffin ma’aikata kuɗaɗen garatutin su da suke bi.

Kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

“Mun gaji basuka daga gwamnatocin baya wanda dole akwai buƙatar a yi nazari da yin tsarin yadda za a fitar da kuɗin domin ya isa guraren da ake buƙata”

Ya ce, tuni kwamitin amintattu na biyan kuɗaden ya fara aikin sa, na yin nazari kan yadda za a raba kuadden ga tsoffin ma’aikata.

Ko da yake bayani kan matsayar gwamnati kan yadda ake zaftare kudaden fansho na tsoffin ma’aikata, Malam Muhammad Garba ya “Ba mu da masaniyar zaftare kuɗaɗaen yan fansho kuma da ma wannan aikin hukumar kula da ƴan fansho ce”.

Kwamishinan yaɗa labaran ya kuma ce, nan bada jimawa ba gwamnatin Kano za ta samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar da suke rayuwa a yankunan karkara.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!