Labarai
Za mu fara hukunta iyayen da ba sa kai yara makaranta- Gwamnatin Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta ce za ta soma hukunta iyaye da masu kula da yara da ba sa tura su zuwa makaranta, bisa tanadin dokar SUBEB ta shekarar 2021.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai-ɗaya ta jihar, Babaji Babadidi, ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamar da gangamin shiga makaranta na shekarar 2025 zuwa 2026 a Amada da ke ƙaramar hukumar Akko a ranar Litinin.
Ya ce dokar ta tanadi hukuncin tara ko zaman gidan Yari na wata ɗaya ga iyayen da suka saɓa, sannan sake aikata hakan na iya kai wa ga zaman gidan yari har na tsawon watanni biyu.
Kwamishinar Ilimi ta jihar, Farfesa Aishatu Maigari, ta bayyana cewa fiye da yara 700,000 ne ba sa zuwa makaranta a Gombe, tana mai jaddada cewa gwamnati na kashe kuɗaɗe sosai a bangaren ilimi, don haka lokaci ya yi da iyaye za su dauki nauyin tura ’ya’yansu makaranta.
You must be logged in to post a comment Login