Labarai
Za mu fara shirin sauya wa tubabbun yan bidiga tunani- Gwamnatin Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa za ta fara wani sabon shiri na koyar da tsoffin ƴan bindiga da suka miƙa wuya, domin sauya musu tunani da kuma koyar da su sana’o’in dogaro da kai.
Shirin, wanda hukumar ilimin manya ta jihar ke jagoranta, zai haɗa da buɗe ajujuwa na karatun boko da na addini, da kuma darussa na faɗakarwa kan illolin kashe mutane da neman fansa.
Daraktar hukumar ilimin manya ta jihar, Bilkisu Muhammad Kakai, ta shaida wa manema cewa nan ba da jimawa ba za a fara aikawa da malamai zuwa ƙananan hukumomi domin koyar da waɗanda suka tuba.
A cewar jami’ar , an kirkiri shirin ne da nufin gyara tunanin matasan da suka shiga harkar ta’addanci, tare da tallafa musu su koma cikin al’umma da rayuwa mai kyau.
You must be logged in to post a comment Login