ilimi
Za mu fitar da biliyan 30 daga asusun tallafawa jami’o’i don inganta ilimi – Chris Ngige
Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara fitar da Naira biliyan 30 don rabawa ga jami’o’in ƙasar nan daga ciki asusun farfado da jami’o’in gwamnati nan ba da jimawa ba.
Ministan ƙwadago da samar da aiki Chris Ngige ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a
yayin wata ganawar sulhu da ta gudana tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU.
A cewar ministan an kira taron ne don kimanta matakin aiwatar da yarjejeniyar fahimtarbjuna da ɓangarorin biyu suka sanyawa hannu a watan Disambar 2020.
Ngige ya ce a yayin taron an gudanar da shawarwari masu gamsarwa tare da tattauna batutuwan da suka shafi ci gaba jami’o’i.
Har ma ya ya ba da tabbacin cewa gwamnati na kan bakanta na inganta tsarin jami’oi don samar da ilimi mai inganci.
You must be logged in to post a comment Login