Connect with us

Addini

Hutun Mauludi: Gwamnatin tarayya ta ayyana Talata a matsayin hutun ma’aikata

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana Talata 19 ga Oktoba, a matsayin ranar hutun ma’aikata don yin murna ga ranar haihuwar Annabi Muhammad (saw).

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya wadda babban sakataren ma’aikatar Dakta Shu’aib Belgore.

Sanarwar ta taya dukkanin musulmi na gida da na kasashen waje murnar bikin wannan shekarar.

Ministan ya gargaɗi ƴan Najeriya da su sanya sanya ƙaunar juna a gaba da hakuri domin su ne halayen Annabi Muhammadu (saw).

Sanarwar ta ci gaba da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!