Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu gyara sansanonin ƴan gudun hijira – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce, za ta yi hadin gwiwa da hukumar kula da ‘yan gudun hijra wajen gyaran sansanonin su a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Yusuf Idris ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau.

Sanarwar ta bayyana cewa, gwamna matawalle yayi wannan jawabi lokaci da ya karbi bakuncin shugabar hukumar kula da ‘yan gudun hijra Hajiya Iman Suleiman a fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Matawalle ya jadda aniyarsa na yin hadin gwiwa da hukumar, wajen gyara guraren da suka lalace karkashin ma’aikatar jin kai da kare abkuwar ibtila’i ta jihar, don fitar da al’umma daga cikin halin da suke ciki fargaba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!