Labarai
Za mu haɗa kai da kamfanoni don samar da filaye da gidaje- Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ce gwaamnatinsa za ta hada kai da kamfanonin da ke samar da filaye da gidaje don saukaka hanyoyin da ma’aikatan gwamnati da kuma sauran mutane masu karamin ƙarfi za su mallaki muhalli cikin sauki.
Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda kwamishinan ma’aikatar gidaje na jihar Ibrahim Adamu Yakubu, ya wakilta yayin bude ofishin kamfanin Mshel Homes.
A nata jawabin, shugabar kamfanin a nan Kano Jamima Boro, cewa ta yi kamfanin yazo Kano ne don sauƙaƙa wa al’umma hanyoyin malakar filaye da gidaje.
Taron bude kamfanin ya samu halartar hukumomin Gwamnati da yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasa da muhalli.
You must be logged in to post a comment Login