Labarai
Za mu haɗa kai da tsofaffin Ƴan Jarida don inganta aikin- Waiya

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da kungiyar yan Jaridu ta kasa NUJ wajen zakulo ma’aikatan Jarida da suka bar aiki a duk inda suke dan amfani da ilimin da suke da shi wajen kara inganta aikin da kuma tsaftace shi.
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da al’amuran cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan, yayin taron masu ruwa da tsaki kan yada labarai daya gudana a nan Kano a wani bangare na taron kungiyar yan Jaridu ta kasa NUJ da yake gudana a nan Kano.
Da ya ke jawabi shugaban kungiyar yan jaridar ta Kasa Alhaji Alhassan Yahaya ya ce za su mayar da hankali wajen shiryawa yan jarida bita kan ayyukan su tare da kare hakkin su a duk inda suke.
Taron ya samu halartar tsoffin shugabannin ma’aikatar yada labarai da masu ruwa da tsaki a fannin inda aka tattauna yadda za a kara inganta aikin.
You must be logged in to post a comment Login