Labarai
Za mu haramta shigo da motoci da aka yi amfani da su sama da shekara 7 – Kwastam
Hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam ta ce ta fara shirye-shiryen daukar matakin haramta amfani da duk wasu nau’ikan motoci wadanda aka yi amfani da su sama da shekara bakwai.
Shugaban hukumar ta kwastam Kanal Hamid Ali mai ritaya ne ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kunshin kasafin kudin hukumar gaban kwamitin kula da hukumar yaki da fasakwauri ta kasa na majalisar wakilai, a Abuja.
Haka zalika shugaban hukumar ta kwastam ya kuma ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta kaddamar da na’urar binciken kwa-kwaf wato scanner guda dari da talatin da biyar a dukkannin tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama da kuma kan iyakokin kasar nan da ke kan tudu.
‘‘Muna ta kokarin bullo da wani sabon tsari da za mu yi amfani da shi wajen rage adadin motoci tuwaris da ake shigowa da su daga ketare’’ a cewar shugaban hukumar ta kwastam.
You must be logged in to post a comment Login