Labarai
Za mu kaddamar da majalisar dattawan da muka samar- Gwamanatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, nan ba da jimawa ba za ta kaddamar da majalisar dattawan jihar da ta samar a shekarar da ta gabata ta 2024 da nufin bayar da shawara ga gwamanati domin ci gaban al’umma.
Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bayyana hakan a zantawara da Freedon Radio, a matsayin jan hankali ga kungiyar tuntuba ta Arewa ACF bisa yunkurin da ta ke yi na kafa sabuwar majalisar dattawan Kano.
Kwamishinan, ya kuma ce, a shirye gwamnatin Kano ta ke wajen hada kai da dukkan wadanda ke da sha’awar bayar da gudunmawa domin ci gaban jama’a ta hanyar bayar da shawarwari.
You must be logged in to post a comment Login