Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan da shekarar 2026 Najeriya za ta samu nasara kan matsalar ’yan bindiga da ta’addanci. Ya yi kira ga ’yan ƙasa da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da ɗaukar nauyin haɗin gwiwa domin magance matsalar tsaro.
Ya bayyana hakan ne a wani taron addu’a da aka shirya a Jihar Akwa Ibom, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya ga ci gaban ƙasa. Haka kuma, ya ce gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa hare-haren da Amurka ta kai kan ’yan ta’adda an yi su ne bisa bayanan sirri da Najeriya ta bayar tare da cikakken amincewar gwamnati.
Akpabio ya ce za’a haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasashen waje, musamman a fannin yaƙi da ta’addanci. Ya buƙaci ’yan Najeriya su ajiye bambance-bambancen siyasa, ƙabila da addini, tare da goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen dawo da tsaro da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login